An Dakatar Da Yajin Aiki Da Zanga-zanga Da Aka Shirya Gabatarwa A Yau Litinin.

Karamin ministan Kwadago Festus Kiyamo ya bayyana haka a shafinsa na Twitter da Facebook cikin Daren yau, Wanda ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya da ‘yan kwadago sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta wucin gadi. Wanda zuwa yanzu Gwamnatin ta dakatar da Karin kudin lantarki na wucin gadi.

Kungiyar kwadago ta NLC tace nanda sati biyu muddin Gwamnatin ta Gaza cimma yarjejeniyar da suka sanyawa hannu to za a tsunduma yajin aiki a kasa baki daya.

Idan Baku mantaba Yau Litinin ne Kungiyar kwadago tayi shirin Shiga Yajin Aikin Gama Gari, bisa Kin Amincewa da Karin Kudin Wutar Lantarki ma man Fetur da gwamnatin Tarayya Najeriya, Karkashin Mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na APC Tayi.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.