Labarai

An daure tsohon Mataimakin shugaban jami’ar Zamfara shekaru 35 a gidan yari bisa samunsa da laifin zamba N260m

Spread the love

Mai shari’a Maryam Hassan Aliyu ta babbar kotun birnin tarayya, Garki, a ranar Alhamis, ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba hukuncin daurin shekaru 35 bisa samunsa da laifin almundahanar Naira miliyan 260.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da shi ne a ranar 12 ga Oktoba, 2021, bisa tuhumarsa da laifuka biyar da suka hada da karbar kudi ta hanyar karya.

Hukumar ta zargi Garba da karbar kudade daban-daban daga hannun wani dan kwangila bisa ba shi kwangilar dala biliyan 3 na shingen bango a jami’ar.

Laifin, a cewar hukumar, ya sabawa sashe na 1 (1) (a) kuma hukuncinsa a karkashin sashe na 1 (3) na dokar zamba da sauran laifuka masu alaka da zamba, 2006.

Alkalin kotun ta samu wanda ake kara da laifukan da ake tuhumarsa da shi kuma ta yanke masa hukuncin da ya dace.

Mai shari’a Maryam Aliyu, ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba, ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a kan zarge-zarge na 1 zuwa 3 da kuma daurin shekaru bakwai a gidan yari a kan zarge-zarge na 4 da 5 tare da zabin tarar Naira miliyan 10 kowanne.

Ripples Nigeria

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button