An haramta anfani da WhatsApp a jihar katsina.

Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarni ga shugabannin makarantun sakandire a faɗin jihar da su rufe kowanne dandalin WhatsApp da malamai suke amfani da shi a makarantun gwamnati.

Kazalika Sanarwar ta bada Umarnin cewa Maaikatan su gujewa yin tsokaci a shafukan Facebook mai ma’ana ko marar ma’ana.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan mataki ne duba da yadda hakan ke kawo ruɗani tsakanin hukumar gudanarwar makaranta da malamai. Daga Muhammad Kabir Aminu

Leave a Reply

Your email address will not be published.