An Jibge ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma A Jihar Ogun Don Dakile Zanga Zangar Dake Shirin Barkewa A Jihar Akan Karin Kudin Fetur.

Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta jibge yan sandan kwantar da tarzoma a jihar Ogun domin fatattakar masu shirin aiwatar da zanga zanga kan nuna kin Amincewa da Karin kudin manfetur Dana wutar lantarki da gwamnatin shugaba Buhari tayi a cikin makon nan.

A ranar juma a ne aka samu wata kungiya me zaman kanta ta gudanar da zanga zanga a garin osun dake kudan cin Nigeria akan Karin kudin manfetur Dana wutar lantarki, gobe asabar kuma wata kungiyar zata gudanar da zanga zangar a jihar Ogun kan kin amincewa da Karin kudaden.

A halin da ake ciki yanzu dai an kai Jami an tsaro cikin lungu da sako da jihar ta Ogun don dakile yunkurin zanga zangar da matasan garin ke shirin farawa kamar yadda wani mazaunin jihar ta Ogun me suna Salihu Abdulkareem yasanar ta wayar salula.

Meye ra ayinku game da wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka kan masu zanga zangar.?

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published.