An kama miyagun ƙwayoyi cikin mutum-mutumin Maryama mahaifiyar Yesu

Masu safarar miyagun kwayoyi sun shiga hannun jami’an NDLEA bayan kama su da aka yi da tarin kwayoyi – Salonsu shine na dankara miyagun kwayoyin a mutum-mutumin Maryama, mahaifiyar annabi Isah

An kama wasu miyagun kwayoyin a cikin safayar bangarorin ababen hawa inda za a tura su Dubai da Canada Masu safarar miyagun kwayoyi dake neman hanyar boye miyagun ayyukan su sun yanke hukuncin ci da addini ta hanyar dankara miyagun kwayoyin a gunkin Maryama, mahaifiyar annabi Isah. Hukumar yaki da safara tare da hana fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama kamfanoni biyu da suka boye miyagun kwayoyi a a gunkin da kuma wasu safayar bangarorin ababen hawa da za a kai kasashen Canada da daular Larabawa.

ADVERTISING An samu sinkin kwayoyin methamphetamine mai nauyin gram 140 da aka zuba a gunkin Maryama wanda za a kaiwa wasu ‘yan kasar Philippine, Daily Trust ta wallafa.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *