An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

An kama wani jami’in sojan Najeriya, Sani Mohammed, da akwati biyu na harsashi 2000, wanda suka tabbatar da lamarin sun shaidawa Premium Times.

Sojan, mai mukamin lance corporal, ya shiga hannu a tashar Maiduguri inda ma’aikatan NURTW suka kama shi lokacin da ya ke shirin hawa mota don tafiya babban birnin tarayya, Abuja.

Kamar yadda majiyar mu ta ruwaito, sojan, wanda ke cikin tawagar jami’ai na musamman 198, an sallame shi daga aiki a Damasak da ke Jihar Borno bayan ya samu rahoton jinya.

Da yan sanda suke tuhumar sa, Mohammed ya ce ya samu harsahin daga wata mota da ta lalace a wajen aikin sa.

Sauran abubuwan da aka samu a wajen Lance Corporal Sani Mohammed bayan harsashi 2000 sun hada da shaidar hutun aiki na kwana uku da kuma takardun gwajin asibiti guda biyu.

Rundunar soji ta ce sojan bai karbi izinin yin tafiya ba.

Wata majiyar sojoji ta ce rundunar soji na jiran hukumar yan sanda ta mika mata jami’in don gudanar da cikakken bincike akan lamarin.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *