An Kama Wasu ‘Yan Bindiga A Hanyoyin Abuja Da Kewaye

A cigaba da kama muggan barayi da masu sace mutane don nemar kudin fansa inda ‘yan sanda sun sake yin wani wawan kamu da kuma hallaka wasu mugga a hanyoyin Abuja da kewaye.

‘Yansanda sun kashe biyar daga cikin wasu mafasan da su ka kashe wani dan sanda jiya a hanyoyin Abuja da garuruwan da ke kewaye. Baya ga nan kuma ‘yan sandan sun damke guda 34 daga cikin wasu masu sace mutane don neman kudin fansa.

Daya daga cikin mafasan mai suna Husaini Mohammed ya bayyana cewa sun samu inifom din soja ne a wajen wani fashi da su ka yi. Ya tabbatar da cewa ya kashi mutum sau daya a wurin fashi da makami a hanyar Lokoja.

Ya ce ya shiga yaki da makamin ne saboda ya na da iyali da yara 10 kuma ya yi ta noma amma ya kasa ciyar da su da noman. Wani kuma mai suna Ibrahim Suleiman wanda y ace shi dan Zariya ne y ace tsautsayi da son zuciya su ka jefa shi cikin fashi da makami. Daya daga cikin ‘yan bindigar ya ce ya sayi bindigarsa wajen Naira dubu 350 ne.

Wani dan fashin kuma ya ce ya kashe dan sanda ne saboda ya fada masu yayin da su ke aiki (wato fashi da makamin shi ne aikin) kuma sun kwace bindigar ‘yansandan.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *