Labarai

An kashe wani Babban jami’in CBN da matarsa har lahira

"Ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma muna da wanda ake tuhuma a tsare," in ji Mista Oyeyemi.

Spread the love

“Ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma muna da wanda ake tuhuma a tsare,” in ji Mista Oyeyemi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kashe Kehinde Fatinoye ma’aikacin babban bankin Najeriya reshen Abeokuta da matarsa ​​Bukola Fatinoye ma’aikaciyar Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Abeokuta (FUNAAB) a unguwar Ibara GRA da ke Abeokuta.

Mahara sun bi sawun Mista Fatinoye da matarsa ​​zuwa gidansu bayan kammala hidimar sabuwar shekara, inda suka kashe su tare da kona gidansu, kamar yadda hukumomin ‘yan sanda suka tabbatar.

Jami’an ‘yan sanda da masu kai daiki na farko ne suka kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.

An ba da rahoton bacewar dan marigayin da ma’aikatan gidansu bayan harin, inda majiyoyin iyalan suka ce wadanda suka kashe sun yi garkuwa da su.

Da yake magana da jaridar The Gazette, kakakin ‘yan sanda a Ogun Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da kisan tare da bayyana cewa an kama wani da ake zargi.

“Ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma muna da wanda ake tuhuma a tsare,” in ji Mista Oyeyemi.

Ya kara da cewa, “Kwamishanan ‘yan sanda ya umarci sashen kisan kai da kuma CID da su hada kai da bincike tare da gaggauta gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button