Labarai

An Raunata Masu Ibada A Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari A Masallacin Jihar Delta A Kokarin Su Na Yin Garkuwa Da Liman

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a jihar Delta da ke kudancin Najeriya a ranar Juma’a, inda suka raunata wasu masallata 11 bayan da suka yi yunkurin yin garkuwa da limamin, in ji ‘yan sanda.

An kai harin da sanyin safiyar a masallacin da ke Ughelli, kusa da garin Warri mai mai.

Kakakin ‘yan sanda Bright Edafe ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP yana mai tabbatar da faruwar lamarin (mutane) 11 sun jikkata.”

Ya ce ana ci gaba da bincike don gano wadanda ake zargin.

Kafofin yada labaran cikin gida da suka rawaito wani shugaban al’umma da kuma wanda abin ya shafa sun ruwaito cewa an yi garkuwa da wani limami a yayin harin.

‘Yan sandan sun yi watsi da ikirarin, suna masu cewa “da nufin daukar shi (limamin) amma su (‘yan bindigar) ba su yi nasara ba.”

Sace-sace dai ya zama ruwan dare a Najeriya kuma ana yin sa ne domin neman kudi ga masu aikata laifuka da aka fi sani da ’yan bindiga wadanda ba su da masaniya kan akida.

Tsaro a jihar Delta ya samu kyautatuwa idan aka kwatanta da farkon shekarun 2000 lokacin da kungiyoyin tsageru suka kai hari wuraren mai ko kuma suka yi garkuwa da ma’aikatan mai.

Sai dai a jihohin kudu maso gabas da ke makwabtaka da kasarnan, an dora alhakin hare-hare da dama a kan haramtattun ‘yan awaren, kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da kuma reshenta masu dauke da makamai, wato Eastern Security Network.

Kungiyar IPOB mai fafutukar neman a ware wa ‘yan kabilar Igbo wata jiha ta daban, ta sha musanta zargin ta da hannu a rikicin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya hau mulki a shekarar 2015 kuma aka sake zabensa a 2019, yana fuskantar matsin lamba kan ya dauki mataki kan matsalolin tsaron Najeriya kafin ya sauka daga mulki bayan zaben da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button