An Samu Nasarar Ceto Mutane 11 Daga hannun ‘yan ta’adda masu Garkuwa A Jahar Zamfara.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya taimaka wajen ceto mutane 11 da yan bindiga suka sace ba tare da kudin fansa ba.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, maza takwas mata uku, sun fito ne daga jihohin Bauchi da Neja da Sakkwato da kuma Zamfara.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun nuna farin cikinsu da kubutar da su, suna bayyana kokarin Gwamnan a matsayin jajircewa tare da tausayin al’ummarsa.

Gwamna Matawalle, wanda ya karbe su a gidan Gwamnatin, ya ba da tabbacin cewa gwamnatin sa ba za ta huta ba har sai an samu cikakken zaman lafiya a jihar.

Ya bayar da umarnin a kai wadanda lamarin ya rutsa da su asibiti don tabbatar da lafiyar su tana cikin kyau kafin daga bisani a hadu su da danginsu.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published.