An yi jana’izar Hajiya Aishatu Ahmadu Bello

An yi jana’izar Hajiya Aishatu Ahmadu Bello, Ƴar Sardaunan Sokoto ta biyu da ta rasu tana da shekara 75.

Marigayiyar tsohuwar matar Marafan Sokoto an yi jana’izarta ta ne a masallacin Sarkin Musulmi da ke jihar.

Hajiya Aisha ta rasu ta bar ƴaƴa da jikoki ciki harda Magajin Garin Sokoto Alhaji Hassan Danbaba.

Mahaifiyar Hassan Danbaba ta mutu ne a ranar Juma’a, a wani asibiti da ke Dubai bayan fama da wata matsagaiciyar rashin lafiya.

Yusuf Dingyade

Yusuf Dingyade
Yusuf Dingyade

Jana’izar ta samu halartar mutane da dama daga ciki da wajen jihar ta Sokoto, ciki har da Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, da tsohon gwamnan Jihar Zamfara Abdul’azeez Yari da Saminu Turaki.

Akwai Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawal da Aliyu Gusau da Sarkin Sudan Shehu Malami da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *