Labarai

An zubda jini a taron masu ruwa da tsakin APC a kano a daidai Lokacin doguwa ya Kaiwa Murtala garo hari da kofin shayi.

Spread the love

A jiya ne Ranar Litinin din da ta gabata ne wani babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a Kano ya rikide zuwa zubar da jini yayin da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Doguwa ya kai wa mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar Murtala Garo hari.

Taron wanda aka gudanar a gidan mataimakin gwamnan jihar Nasir Gawuna, an shirya shi ne domin duba nasarori da gazawar da aka samu a ziyarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Mista Doguwa, wanda ba a gayyace shi taron ba, ya je ganin shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas.

AN  tattaro cewa Mista Doguwa ya damko kofin shayin mataimakin gwamnan ya jefawa Mista Garo.

Wakilinmu ya tattaro cewa a kokarin da ya yi na dakile harin da hannunsa, tarkacen kofin gilashin ya bugi Mista Garo a hannunsa kuma ya raunata shi.

Sai dai taron ya kare bayan faruwar lamarin, inda mataimakin gwamnan ya gargadi Mista Doguwa da ya fice a gidan sa.

Kafin faruwar lamarin a ranar litinin, DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Mista Doguwa ya zubawa kwamishinan yada labarai na jihar, Mohammed Garba, forwser bayani a karo na gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button