ANTUNA DA WATA MOTA: Wannan mota ce dake dauke da na’uran sautin gwagwarmaya na gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a fagen siyasa (Tandara) wanda tun lokacin yakin neman zaben sa shekaru 2 da suka wuce take bada gudumawa.

Kamar yadda aka saba wannan Karon ma anyi amfani da ita wajen taron cika gwamnatin sa shekaru biyu amma Allah cikin ikon sa yau tsautsayi ya sa ta Kone qurmus Jim kadan bayan an tashi daga taro sanadiyar kamawa da wuta da na’uran janareta dake kan motar yayi saboda zafi da ya dauka yayin gudanar da taro a filin wasa na Pantami.

Kodayake akwai yunquri da al’umma dake ganau ne a wajen sukayi wajen amfani da hodar kashe gobara (fire extinguisher) don kashe wutar amma abin ya ci tura.

Duk da jami’an hukumar kashe gobara sun kawo nasu gudumawan don kashe wutar amma dai qaddara ta riga fata.

Abdul No Shaking
Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Gombe a Sabbin Kafafen Sadarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *