Labarai

Ashe Uwa Bazata Ƙara Ganin Ɗan taba: Mahaifiyar Dadiyata ta Rigamu Gidan Gaskiya.

Spread the love

Allah yayiwa Malama Fatima Rasuwa, Mahaifiya ga Abubakar Idris (Dadiyata). Hakan na biyo bayan wani rashin lafiya mai tsanani da tayi fama dashi. Inda ta rasu ranar talata a wani asibiti dake can asibitin sojoji na 44.

Malam Muhammad wani bawan Allah ne da yake da kusanci da iyalan Dadiyata, ya shaidawa majiyar Jaridar Mikiya cewar, da asubahi aka garzaya da ita zuwa asibiti, bayan jikin nata ya yi tsanani.

Kamar yadda jaridar Daily Trust Hausa ta ruwaito, akwai wani Malam Kawali amini ga Dadiyata, ya shaida mata cewar, ƴaƴanan marigayiyar na kan hanyarsu ta komawa Kaduna, bayan samun labarin rasuwarta.

Dadiyata dai an sace shine a 1 ga watan Augusta na 2019, babu shi babu labarin sa. Sai gashi ana batun ɓatan nasa, ya rasa mahaifiyar sa.Allahu Akbar ashe Ashe Uwa Bazata Ƙara Ganin Ɗan taba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru qa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button