Labarai

Atiku ya koma Kasar Dubai wajen amaryarsa Balarabiya dake zaune a kasar ta Dubai.

Spread the love

Atiku dai ya yi kaurin suna wajen kwashe mafi yawan lokutan sa a Dubai bayan INEC ta ayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben 2019.

A ranar Juma’a ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai fara wata tafiya zuwa Turai.

A karshen ziyarar tasa a Turai, tsohon mataimakin shugaban kasar zai kuma ziyarci iyalansa a Dubai, in ji Paul Ibe, mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai.

Tafiyar dai na zuwa ne kimanin makonni uku bayan da Abubakar ya gana da Nyesom Wike, gwamnan Rivers a birnin Landan.

A cewar Ibe, wannan tafiya ci gaba ce ta kasuwanci da tun makonni uku da suka gabata.

Sanarwar ta kara da cewa, “Zai yi tafiya ne nan take bayan ganawarsa a ranar Juma’a a Legas, tare da jagorancin kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta,” in ji sanarwar.

“Tafiyar ta yau na ci gaba da tafiya kasuwanci a baya na makonni uku da suka gabata.

“A karshen tafiyar tasa a Turai, tsohon mataimakin shugaban kasar zai kuma yi amfani da damar wajen ziyartar iyalansa a Dubai.

“Tafiyar sa don kasuwanci ne da dalilai na dangi kuma ba shi da alaƙa da likitocin kamar yadda ake ya’dawa.

Atiku dai ya yi kaurin suna wajen kwashe mafi yawan lokutan sa a Dubai bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben 2019.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button