Labarai

Ba don Kwankwaso ba da yanzu an kashe ni kafin zaben 2015 ~Cewar Shugaba Buhari.

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda wata mota mai sulke wacce tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya ba shi, ta taimaka masa ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hari da aka kai masa jihar Kaduna.

A cikin wani shirin mai suna ‘Essential Muhammadu Buhari’ da aka watsa a ranar Lahadi, shugaban ya bayyana wani lamari da ya kusan kashe rayuwarsa a lokacin yakin neman zaben 2014 kafin ya ci zabe a 2015.

Da kyar ne dai Mista Buhari ya tsallake rijiya da baya sakamakon tashin bama-bamai da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a unguwar Kawo da ke Kaduna, inda ya yi amfani da motar sulke da tsohon ministan tsaro, Kwankwaso, kuma a halin yanzu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ba shi.

Sama da fararen hula 80 ne rahotanni suka ce sun mutu a tagwayen bama-bamai da Buhari, wanda a lokacin dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, ya tsira a ranar 23 ga Yuli, 2014.

Kafin tashin bama-baman, Mista Buhari ya tuna cewa, Kwankwaso ya gargade shi da cewa wadanda ba sa son ya samu mulki na iya sanya shi a matsayin wani mummunan Abin hari. Shugaban ya ce zai iya rasa ransa a yanzu da bai saurari Mista Kwankwaso ba.

“Ina jin Kwankwaso yana kyauta; ya ba ni mota kirar Land Rover mai sulke,” in ji shugaban ya bayyana wa ‘yan Najeriya a cikin shirin. “Ya ce ya kamata in yi amfani da shi saboda ya yi imanin gasar da zan shiga ta hada da mutanen da za su so su kawar da ni.”

Ya ci gaba da cewa: “Ina zuwa Kano daga Kaduna a cikin waccan motar kirar jeep sai wata mota ta so ta riske mu amma rakiyata ta tare su suka tayar da bam din.

“Da na duba, sai na ga guntun mutane. Babu daya daga cikin mu da ya ji rauni a cikin motar. Amma ko ta yaya na ga jini a kaina saboda yawan mutanen da bam din ya kashe a waje.”

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar bayan faruwar lamarin, Mista Buhari ya bayyana cewa yunkurin kisan gilla ne kuma ya bayyana yadda dan kunar bakin waken ya yi kokarin aiwatar da wannan mummunan aikin.

Buhari ya tsaya takara kuma ya sha kaye a zabukan shugaban kasa guda uku kafin daga bisani ya zama shugaban Najeriya a 2015 bayan nasarar da ya samu a zaben shekarar.

A cikin shirin na tsawon mintuna 50 na rayuwar shugaban kasa mai mulki, dan uwansa, Mamman Daura, ya yi ikirarin cewa an matsa wa Buhari lamba kan ya jagoranci gwamnatin Najeriya amma ya yi ta turjiya sau da dama kafin ya fito a shekarar 2002.

Nan gaba ne dai tsohon shugaban kasar zai mika mulki bayan babban zabe mai zuwa. Ya yi alkawarin marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC, Bola Tinubu goyon baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button