Labarai

Ba na jin daɗin rayuwa – Attajiri Alhaji Aminu Dantata Mai shekaru 91

Spread the love

Aminu Dantata, tsohon shugaban hukumar kula da fulawa ta Arewacin Najeriya (NNFM), ya ce ya daina jin dadin rayuwa.

hamshakin dan kasuwan mai shekaru 91 ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC da Abdullahi Ganduje, gwamnan Kano, suka kai masa ziyara a gidansa.

Ya cika shekaru 91 a watan Mayu.

Dantata ya ce ya zagaya duk jihohin kasar nan kuma ya yi abota da yawa, inda ya ce da kyar ya iya tantance guda 10 da ke raye.

Ya bukaci mutanen da ya yi wa laifi su yafe masa ya kuma ce ya yafewa duk wanda ya bata masa rai.

“A gaskiya, ni kadai ne ya rage a cikin iyalina da ke zaune tare da jikoki,” in ji Dantata.

“Allah kada ya barmu da kokarinmu kadai. Muna addu’ar Allah ya ci gaba da yi masa jagora da kariya”.

Dattijon ya nuna jin dadinsa ga Kashim Shettima da Abdullahi Ganduje bisa wannan ziyara da suka kai masa, ya kuma yi addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya a kasar nan.

Thecable

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button