
A Lokacin da take rubuta Sakon godiya a shafinta na Facebook ga tarbar da akayi Mata a kasar India Jarumar Rahma sadau tace
Tabbas Ina matukar murna da godiya ga daraktocin masana’antar fina-finan kasar India da suka saka ni na kera sa’a na zama tauraruwar kasa da kasa Kun cikamin mafarkina na dogon Lokaci ba Zan iya biyanku ba Kan wannan Farin Ciki da kuka kawo cikin rayuwa ta na Sami Karin Ilimi kune Mutane mafi girma da kyawu da nayi aiki a tare dasu aduk tsawon rayuwata, yanzu addu’a ta shine Cigaba da kulla abota ta har’abada,
Jaruma Rahama sadau na ‘daya daga cikin Jerin fitattun jarumai Mata a masana’antar fina-finan Kanywood dake arewacin Nageriya Kuma Yanzu Haka Jarumar na can kasar India domin ‘daukar wani sabon Mai suna Khauda Haafiz.