Labarai

Ba zan yarda na rasa kuri’un talakawan jihohin Kano katsina Kebbi da sauran jihohi hu’du a arewacin Nageriya ba ~Cewar Bola Tinubu.

Spread the love

A daidai lokacin da ake ta cece-kuce gabanin zabukan 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu na kulla kawance da wasu gwamnonin Arewa masu barin gado domin samun kuri’u a yankin.

A filin wasa na Teslim Balogun da ke jihar Legas a yau ranar Asabar yayin wani gangami, Tinubu ya yi alfahari da cewa kawancen da ya yi da gwamnonin Kano da Katsina da Kaduna, da Kebbi, da Kwara, da kuma Filato za su ba shi mafi yawan kuri’un da ya ke bukata domin samun nasara kan ‘yan adawa da suka hada da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP), da Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Kalaman na Tinubu na zuwa ne watanni biyar bayan kimanin gwamnonin Arewa 10 suka goyi bayan takararsa a zaben fidda gwani da aka gudanar a watan Yuni.

“Shin za ku iya ganin gwamnonin Kano, Katsina, Kaduna, Kebbi, Kwara, da Plateau?” Tinubu ya tambayi dimbin magoya bayan jam’iyyar APC.

“Ba za mu rasa ko daya daga cikin jihohin ba. Za mu yi mulkin kasar nan tare. Suna nan Legas don nuna goyon bayansu a gare inji Bola Tinubu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button