Ba zan yarda ‘ya ‘ya na su fita zuwa kasar waje ba dole mu zauna a nan domin bamu da Kamar Nageriya ~Cewar Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku, ya ce duk da wahalhalun da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke ciki a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buharia, ‘ya’yansa ba za su fita zuwa wasu kasashe ba.

Atiku ya bayyana haka ne a wani taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na Kudu maso Gabas a Enugu ranar Talata.

A halin da ake ciki, Atiku ya ba da tabbacin cewa zai ba da fifikon ci gaban jarin dan Adam da ingantaccen ilimi don baiwa matasa damar yin gogayya a kan tattalin arzikin zamani.

Atiku ya ce, “A gwamnatin da na yi mataimakin shugaban kasa a cikinta, ka ga ‘yan Najeriya sun dawo daga kasashen waje don zuba jari a wasu damammaki a kasar.

Lokacin da na tabbatar na samar da ka’idojin kasa da kasa, yawancin ‘yan Najeriya daga Amurka da Turai sun dawo sassan Nageriya ba iya Legas ko Abuja ba harma zuwa Yola Arewa maso Gabas. Suka dawo. Abin da ya kamata mu yi shi ne mu tabbatar mun sanya kasarmu ta zama abin sha’awa don dawowar su kuma za su dawo,” ya kara da cewa.

“A karkashin jam’iyyar APC, lamarin ya koma baya. Mutane ba za su iy jira suna gudu daga Najeriya kuma Dukansu suna da dangi, yaran da suke gudu zuwa Amurka, Kanada Nima Ina da nawa Amma naki yarda daya daga cikinsu ya fita waje ya zauna a gida saboda ban yarda ba. Dole ne mu zauna a kasar nan.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi alkawarin zai tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga jama’a.

“Za mu kuma samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya wanda ke mai da hankali kan kula da rigakafi. 

Don haka za mu ba da jari mai yawa a wannan yanki mai mahimmanci. Ingantacciyar ma’aikata mai ilimi da lafiya tana da mahimmanci ga tattalin arziki da samar da wadata a duniyar yau,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *