Babban ‘Dan Marigayi Sheikh Jafar Adam, ya samu jariri, ya sa masa suna Jafar

A ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, 2021, Malam Salim Jafar Mahmud Adam ya bada sanarwar cewa Mai dakinsa ta haihu.

Wannan Bawan Allah ya samu baiwar ‘diya mace ne a daidai ranar 28 ga watan Ramadan, 1442.

A daidai lokacin da musulmai su ke shirin bankwana da watan Ramadan, sai aka ji Salim Jafar Adam ya samu karuwar namiji.

Salim Jafar Adam wanda shi ne babban ‘dan Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam, ya bada wannan sanarwa a shafin Twitter.

“Alhamdulillahi…Allah ya albarkacemu da jariri namiji (sunansa Ja’afar Ibn Saalim);” inji Salim a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

“Da jaririn, da mahafiyarsa, duk suna cikin koshin lafiya. Muna barar addu’o’i wajen saukin samun lafiyar mahaifiyar jaririn.

Daga baya, Salim ya yi wa jama’a godiya da irin addu’o’in da suka rika yi wa iyalinsa, da kuma mahaifinsa wanda ya yi wa takwara.

“Assalamu alaikum, Nayi farin ciki matuka bisa ga addu’o’inku, da fatan Alheri, akan karuwa da muka samu, Allah ya saka muku da alheri.

“Allah ya amshi addu’o’inmu baki daya. Allah Ya kara Jikan malan, Ya kai rahama makwancinsa, Ya hada fuskokinmu baki daya a Aljannar firdaus.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *