Labarai

Babu abinda ba zamu iya yi don kare mutunci masarautarmu ba.” Don haka mun baiwa kamfanin Air Peace kwanaki 3 ta baiwa Sarkin Kano Hakuri, |~ Inji Masarautar Kano

Spread the love

Daga | Ahmad Aminu Kado,

Shugaban tsare-tsare na masarautar Kano, Isah Bayero, ya baiwa Air Peace sa’o’i 72 su baiwa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, hakuri bisa wulakantashi da suka yi da jinkirta tafiyarsa.

Malam Isah Bayero ya bayyana hakan ranar Asabar yayin hira da wasu manema labarai a jihar Kano,

Yace wajibi ne kamfanin Air Peace ya amsa cewa yayi laifi wajen kin bin tsari, wanda haka ya sabbaba jinkirin Sarkin Kano a tashar jirgin Legas.

Yace: “Tunda mun yi jinkirin barin Banjul da awa guda, ya kamata su sani da akwai fasinjoji goma dake niyyar zuwa Kano kuma suyi abinda ya kamata saboda ba laifinmu bane jinkirin da ya faru.”

“Na kirasu sau da dama amma suka ki daukan waya sai daga baya sukace ba zai yiwu ba.Ya kamata shugabannin kamfanin su rika yiwa manyan mutane shiri na musamman.”

“Tun da sun jinkirta tashinmu daga Banjul, wanda ya sabbaba jinkirin zuwa Legas, ya kamata Air Peace ya shirya yadda za’a damu. Amma babu abinda sukayi.”

“Ina basu sa’o’i 72 su baiwa Sarki hakuri, na farko a jarida, na biyu kuma su turo wakilai wajen Sarki. Babu abinda ba zamu iya yi don kare mutunci masarautarmu ba.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button