Babu Nakasashshe Sai Rago: An hango wani kurma yana tuƙa adaidaita sahu a Lagos (Hoto).

Kurma Direba

Ita rayuwar nan a koda yaushe cike take da abubuwan almara iri iri. Wani lokacin su baka haushi, tausayi, dariya, wani lokaci kuma su saka kayi kasaƙo, kana tunanin me zakayi saboda kiɗima, mamaki, ko kuma furgita da abin ido yagani, kunne yaji wanda ba kasafai aka cika ji ko gani ba.

Kwarai kuwa, wannan shine abinda ya faru a garin Lagos, yayin da aka hango hoton wani kurma yana tuƙa adaidaita sahu, inda yake ta zazu da mutane ko a jikinsa.

Kai idan baka sani ba, sai ka zata tabbas, wannan mutumin yana da kunne.

Wannan hoto na kurma, yaja hankalin jama’a sosai , wanda saboda haka ne ya zama abin ambato da zantawa mafi fice a kafafen sada zumunta na zamani.

A hoton da yake ta zagayawa a kafafen sada zumunci na zamani, an hango umarni da wannan kurma direba ya rubuta.

Kurma Direba

Kamar yadda aka gani a hotan dake sama, abune ƙwaraƙwatan cewa shi mai tuƙin kurma ne, ya rubuta saƙo mai jan hankali da yake nuni ga wanda yahau babur ɗin cewa, shifa kurma ne, saboda haka a taɓa shi, idan aka isa gurin da za’a sauka ko kuma idan ana so a biya kuɗin babur.

Ga abinda saƙon yace a cikin yaren bature mai jan kunne:

Ni kurma ne, don Allah a taɓa ni, idan za’a tsaya ko za’a biyani kuɗina. Nagode”

Kalli hoton a ƙasa:

Kurma direba

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *