Babu wata kalar barazana da zata bani tsoro Kuma ta hana na zama Shugaban kasar Nageriya ~Inji Bola tinubu.

Tsohon Gwamnan Jihar Lagos ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Bola Tinubu, a ranar Lahadi, ya sha alwashin cewa babu wata barazana da za ta iya hana shi takarar shugaban kasa a 2023.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da Olubadan-designate, Oba Lekan Balogun.

A watan Janairu ne Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana masa shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023.
Da yake jawabi a fadar Olubadan da ke Ibadan, shugaban jagoran APCn na kasa ya dage cewa babu wani abin tsoro da zai hana shi cika burinsa.

Ya ce ziyarar da ya kai Oyo da Ibadan ta biyo bayan mutunta kujerar sarauta, da kuma neman albarkarsu da hadin kai da kuma addu’o’in samun shugabancin kasar nan a shekarar 2023.

Ya ce: “Babu wani abin tsoro da zai hana ni. Na shirya daukar duk wani bakin jini da Zan zama shugaban Najeriya.

One thought on “Babu wata kalar barazana da zata bani tsoro Kuma ta hana na zama Shugaban kasar Nageriya ~Inji Bola tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *