Bafarawa ya mikawa Shugaban Majalisar wakilan Nageriya kundin biyan diyyar ‘yan Arewa.

Bafarawa Ya Mikawa Kakakin Majalisar Wakilai Kundin Korafin Barnar Da Aka Yiwa ‘Yan Arewa, Na Kimamin Tiriliyan 7, Domin A Biya ‘Yan Arewa Asarar Barnar Da Aka Musu, A Lokacin Zanga-zangar #ENDSARS

…..Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” ta na jinjinawa Alhaji Attahiru Bafarawa, kan namijin kokarin da yake yi wajen ganin an biya dukkanin al’ummar Arewa diyya kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka musu.

Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”

Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, tana jinjinawa tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa, kan namijin kokarin da yake yi wajen ganin an biya ‘yan Arewa diyya kan asarar rayuka da dukiyoyi masu dunbun yawa da akayi musu a yayin zanga-zangar #ENDSARS a kudancin Nijeriya.

Bayan jagorantar tattara bayanan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yiwa al’ummar Arewa, nan take Bafarawa ya mika rahoton sa ga kakakin majalisar wakilai Hon. Femi Gbajabimiala don bin kadin haqqoqin al’ummar yankin Arewa da kuma neman biyan diyya wanda jimlar sa takai Naira Tiriliyan 7.

Idan ba’a manta ba Gbajabiamila shine wanda ya ce ba zai sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2021 ba, inhar ba’a hada da batun biyan diyya ga mutanen da ‘yan sandan SARS su ka yi wa illa a kudancin Nijeriya ba.

Kungiyar “Arewa Media Writers” tayi matukar farin ciki da samun jajirtaccen shugaba mai kaunar yankin Arewa a dai-dai wannan lokacin da kowa ya juyawa al’ummar yankin baya, babu shakka wannan babban abin farin ciki ne garemu da duk wani ‘dan Arewa mai kishin yankin.

Kungiyar “Arewa Media Writers” tana yiwa Alhaji Attahiru Bafarawa, addu’ar fatan alkhairi tare da goya mashi baya kan wannan yunkurin da yayi na ganin ya share hawayen dukkanin al’ummar yankin mu na Arewa.

Haka zalika kungiyar “Arewa Media Writers” a shirye take da ta bada gudummuwar ta, ga dukkanin wani abu da za’a aiwatar don kawo wa yankinmu na Arewa cigaba.

Fatan Kungiyar “Arewa Media Writers” Allah ya bawa Alhaji Bafarawa, sa’a kan wannan jan aiki da yasa a gaba, wanda wasu daga cikin manyan yankin namu suka kasa.

Rubutawa:
Bashar M Bashar
Chairman Arewa Media Writers Sokoto Chapter.

Leave a Reply

Your email address will not be published.