Labarai

Bamu da zabin wani da zai Zama shugaban kasar Nageriya mu kowa namu ~Cewar Gwamnatin London.

Spread the love

Gwamnatin Birtaniya ta ce ba ta da sha’awar wanda zai zama shugaban Najeriya a zaben 2023.

Babbar jami’ar Birtaniya a Najeriya, Catriona Liang, ce ta bayyana hakan a ranar Laraba bayan wata ganawar sirri da ta yi da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa, NWC, a Abuja.

Misis Liang ta yi nuni da cewa, Masarautar za ta yi aiki da duk wani dan takarar da ya fito, inda ta bayyana amincewa da dimokuradiyyar Najeriya da kuma kudurin shugaban kasar na yin zabe cikin kwanciyar hanka da lumana

Ta ce: “Wannan taro daya ne da nake yi da jam’iyyun siyasa, da ‘yan takarar shugaban kasa, da kuma shugabannin jam’iyyar. Kuma a yau ne shugaban jam’iyyar APC ya isar da sakon mu game da babban zabe.

“Muna maraba da kudurin Najeriya na tabbatar da dimokuradiyya da kuma kudurin shugaban kasa na tabbatar da zabe mai inganci.

“Mun yi magana kaɗan dalla-dalla game da yanayin da ya dace don hakan ya faru. Da kuma damuwa game da rashin tsaro.

“Sannan kuma muhimmancin fitowar jama’a a wannan rana da kuma karfafa wa mutane da dama yin rajista domin suna bukatar fitowa zabe a ranar zabe.

“Hakan yana nufin babu tsoro da ingantaccen muhalli. Kuma mutane na ganin za su iya zaben dan takarar da suke so.

“Birtaniya ba ta da wanda taka fi so. Mun himmatu wajen gudanar da sahihin zabe, amma za mu yi aiki da duk Yan takarar shugaban kasa a zaben.

“Birtaniya da Najeriya suna da kawance mai karfi, kuma muna son Najeriya ta yi nasara. Kuma dimokuradiyya tana cikinta”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button