Ban yarda Cewa ‘yan Siyasa ne Suka kashe Ahmad Gulak ba ~Inji Gwamna Wike.

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce takwaransa na jihar Imo, Hope Uzodinma ya yi hanzarin bayyana cewa mutuwar jigon APC, Ahmed Gulak kisan gilla ne na siyasa.

A wata sanarwa da aka watsa a ranar Litinin, Gwamna Uzodinma ya nuna kaduwa game da kashe jigon na APC, yana mai bayyana lamarin a matsayin mummunan lamarin kisan gilla na siyasa, ra’ayin da Gwamna Wike bai aminta ba.

Yayin da yake bayyana a matsayin bako a gidan talbijin na Channels a Shirin Politics today, Wike ya ce kamata ya yi takwaransa na Imo ya yi haquri tare da ba jami’an tsaro damar yin aikin da aka kafa su kafin ya yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *