Labarai

Ban yi murabus ba – Ministan Shari’a Malami.

Spread the love

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, (Dr.) Abubakar Malami, SAN ya sake karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ya yi murabus.

Yayin da yake karyata jita-jitar ta wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja, Malami ya ce, “Ban yi murabus ba.”

Dokta Umar Jibrilu Gwandu, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, ya ci gaba da cewa, Malami yana ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da kundin tsarin mulki ya tanada kamar yadda wasu dokoki suka tanada.

Don haka Malami ya godewa ‘yan Najeriya bisa nuna soyayya da sha’awar da ba ta misaltuwa a gare shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button