Labarai

Bana tare da layin tafiyar Atiku amma Ina tare da layin tafiyar Gwamna Nyesom Wike.

Spread the love

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce tare yake da tawagar Gwamna Wike na jihar Rivers.

Majiyarmu ta DKC tace Gwamna Bala Mohammed na magana ne a Bauchi a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Gwamna Wike.

Rikici dai ya dabaibaye jam’iyyar PDP a yayin da take neman darewa guda biyu, tsakanin masu goyon bayan Gwamna Wike da masu mara baya ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Mekinde ne kadai bai halarci zaman ba a Bauchi, shi ma rahotanni sun ce ya yi tafiya zuwa kasar waje. Amma dai taron ya samu halartar Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da Samuel Ortom na jihar Benue da Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Gwamnan Bauchi ya ce baya wani baye-boye, yana tare da wannan tawaga mai lakabin G6 da Gwamna Wike ke jagoranci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button