Banda wani buri a yanzu da ya wuce na ga bayan ‘yan ta’adda a kowace kusurwa ta Najeriya~ Inji Janar Faruku Yahaya

A yau Litinin, sabon shugaban Hafsan sojin Najeriya Janar Faruku Yabaya ya bayyana cewa a yanzu baida wani buri da ya wuce ganin ya hallaka ‘yan ta’adda a kowace kusurwa ta Najeriya.

Janar Faruku Yahaya ya bayyana hakan ne a yau Litinin a lokacin da ya kira taron manya Hafsoshin sojin Najeriya ne domin fuskantar matsalolin tsaro da Najeriya take ciki.

A cikin jawabin sa, Janar Faruku Yahaya ya yi kira ga manyan Hafsan sojin Najeriyar da su tashi tsaye haikan don ganin an magance matsalar tsaro a kowace kusurwa ta Najeriya.

Faruku Yahaya ya ci gaba da cewa” Insha Allahu zan ci gaba daga inda marigayi Attahiru Ibrahim ya tsaya na aiki tukuru don ganin an kawo karshen ta’addanci a Najeriya”.

“Saboda haka insha Allah karkashin jagoranci na rundunar sojin Najeriya zata yi aikin tukuru domin ganin mun sauke nauyin da shugaba Buhari ya dora mana ta hanyar kawo karshen matsalar tsaro a kowace kusurwa ta Najeriya”. Inji Faruku

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *