Labarai

BASHIN 10bn: Ganduje na shirin ruguza rayuwar ‘ya ‘yan mu na jihar kano da bashi ~Cewar Jam’iyar NNPP

Spread the love

Sabuwar jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP),     ta yi tir da sabuwar buƙatar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na buƙatar  rancen Naira biliyan 10 daga Bankin Access don girke kyamarar CCTV a jihar.

Jam’iyyar NNPP a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta na Kano, Umar Haruna Doguwa ta ce “ba za ta iya zura ido tana ji tana kallon wannan gwamnati maras hankali ba tana tara basussuka a jihar ba tare da samun kwakkwaran nasara a kasa ba.

Ga dukkan alamu Gwamna Ganduje yana amfani da kujerarsa wajen jingina makomar jihar da ta yaran mu.

Sakamakon gazawar gwamnatin Ganduje na biyan kudin jarabawar manyan makarantun sakandire, dalibai da dama ne aka tilastawa barin makaranta wasu kuma na gab da rasa karatunsu.

Yayi watsi da yadda jihar ke fama da matsalar karancin ruwa, gwamnan ya zabi ya ci bashi don daukar nauyin aikin da bai taka kara ya karya ba kamar na’urar CCTV.

jama’a sun tuna cewa a baya, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mu, Engr, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya tura CCTV a wurare masu muhimmanci a fadin jihar.

Sai dai kuma gwamnati mai ci da ke neman rancen Naira biliyan 10 don girka sabbi ta kasa sarrafa su, kuma mutanen Kano nagari ba za su amince gwamna ya kafa sabbin ba wanda za yi musu illa.

Babbar jam’iyyar mu tana kira ga majalisar dokokin jihar da ta daina biyan kananan bukatu daga gwamna musamman irin wadannan.

Muna kira ga ‘yan uwa da su sanya bukatun mutanen Kano nagari a gaba da rashin gamsuwa da burin gwamna na ruguza makomar jihar kafin mu kayar da su a zaben 2023.

Haka nan muna kira ga bankin Access da ya bijirewa duk wani rancen da zai baiwa Gwamna Ganduje da ya ci bashi wanda ke nakasa makomar jihar domin biyan bukatun kansa.

Jama’ar Kano za su iya tunawa sarai cewa Ganduje ya ciyo bashin Naira biliyan goma sha biyar kan gyaran ilimi amma an karkatar da kudin zuwa wani abu kuma a yau din nan sai ga dimbin dalibanmu sun daina zuwa makaranta saboda gwamnati ba za ta iya daukar nauyin jarabawar su ba. jarrabawar babbar sakandare.

Ana kyautata zaton cewa wannan kudi naira biliyan goma (N10b) da majalisar dokokin jihar ta aminta a baya-bayan nan, na nufin biyan wasu makudan kudade da aka karkatar da su da gangan a lokacin zabukan fidda gwani na jam’iyya mai mulki.

Da wannan bayanin, muna so mu ja hankalin dukkan bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin bayar da lamuni na kudi a ciki da wajen kasar nan da su yi taka-tsan-tsan da bukatar Gwamna Ganduje na neman lamuni domin ko ta yaya gwamnati mai zuwa ba za ta mutunta irin wannan rancen gaggauwar ba. inji Shugaban jam’iyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button