Bashin da ke kan Najeriya ya karu sosai a cikin shekara 10, cewar masanin tattalin arziƙi sarkin Kano Sunusi na II.

Tsohon Sarkin Kano ya ce bashin da ke kan Najeriya ya karu sosai a cikin shekara 10

Muhammadu Sanusi II ya ce alkaluman kason bashin wajen Najeriya da kudin da kasar ta ke samu ya tashi da sama da 400% daga shekarar 2011 zuwa 2020.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa da ya ke wani bayani a ranar Alhamis, tsohon gwamnan na bankin CBN, ya koka a kan kudin da ake bin Najeriya bashi.

Sanusi Lamido Sanusi kamar yadda aka san shi a baya ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi magana da shi a wata tattaunawa da Heinrich Böll ta shirya.

Malam Muhammadu Sanusi II ya ce alkaluman CBN sun nuna cewa kudin shigan da aka samu daga haraji a Najeriya a 2011 ya kai kusan Naira tiriliyan 19. Sanusi II ya ce a wancan lokaci duka-duka bashin da ake bin Najeriya bai zarce 10% na kudin da kasar ta ke samu ba, sai dai yanzu, ya ce lamarin ya sake zani.

“Zuwa 2020, kasashen waje na bin mu bashin kusan $33.4b, kuma abin da mu ka iya samu a 2020 kusan $8.3b ne, mun tashi daga 8% a 2011, zuwa 400% a 2020.” Tsohon Sarkin na Kano ya ce alkaluma sun nuna cewa Najeriya ta na cikin hadarin bashi, musamman ganin yadda kudin da ake samu daga mai ya ke yin kasa.
Masanin tattalin arzikin ya ce karfin biyan bashi ba a GDP yake ba, ya ce idan mafi yawan mutane ba su biyan haraji, gwamnati za ta iya fada wa cikin taurin bashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *