Shugaban Nageriya Mohammadu buhari yace Muna aiki tukuru don ganin yanayin tsaro a kowane bangare na Najeriya zai inganta ba da jimawa ba. A matsayinmu da kokarinmu, muna saka hannun jari sosai wajen samo kayan aikin zamani.
Wasu sun iso, wasu kuma suna a tashar Jiragen ruwa, kuma muna da wasu kuma suna kan hanyarsu.
Gwamnatinmu tana iya bakin kokarin ta kan batun kayan aiki, kuma sojoji suna sane Mun fahimci mahimmancin shirya ma’aikatanmu yadda ya kamata,
domin su iya isar da iyakar abin da suke yi. Ina neman wani dan lokaci tare da sayan kayan aiki,
musamman domin bin ka’idar Covid-19 Sannan idan kayan aiki sun isa, muna buƙatar horar da ma’aikata don amfanin su, kafin tura su zuwa filin yaki. Ina son dukkan ‘yan Najeriya su natsu da cewa muna yin iya kokarinmu a wannan batun. Nan gaba za ku ga ingantaccen ci gaba. Tsaro na rayuka da dukiyoyin jama’ar Najeriya zai ci gaba da zama fifiko a garemu.