Labarai

BATUN TSRO: Allah yasa ‘yan nageriya su aminta su yafe mana amma gaskiya lamarin mu akwai ganganci ~Cewar Sanata Babba kaita.

Spread the love

Sanata Mai wakiltar Mazabar shiyyar daura a Jihar Katsina Sanata Ahmad Babba kaita ya bayyana Gwamnatin su ta APC wacce Shugaba Muhammadu Buhari ke Jagoranta amatsayin Gwamnatin ganganci Sanata ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook a lokacin da yake mayarda martani ga maganar da Gwamnan jihar kaduna Malam Nasir Ahmad El Rufa’i yayi na Cewa a dole ne mu roki afuwarku da gafararku domin a gwamnatance mun kasa.

Sanatan dauki maganar ta El rufa’i ya Saka a shafinsa na Facebook ya Kuma Kara da tasa maganar Yana Mai cewa Allah yasa su yadda su yafe malam domin harkar tamu akwai ganganci.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na fama da shan sukar ‘yan nageriya musamman a daidai wannan lokaci da Babban zaben 2023 ke karatowa Yan nageriya na kallon Gwamnatin Shugaba Buhari amatsayin Gwamnatin data Gaza magance matsalar tsaro a nageriya musamman arewacin na nageriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button