Bauchi: Sarki ya dakatar da Wakilin Birni saboda fin shi walkiya a hawan sallah

Sarkin Rilwanu Sulaiman Adamu na jihar Bauchi ya dakatar da Wakilin Birnin Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi, bayan hawan sallah.

An gano cewa Sarkin yayi haka ne saboda tsabar adon da mai sarautar ya caba cikin Alkyabba da Kandiri, wacce ta zarta ta sarkin.

Duk da dai a wasikar dakatarwan an sanar da cewa an dade ana ja wa Wakilin Birni kunne, ya ki gaida Gwamna yayin hawan sallah.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *