Labarai

Bisa zargin damfarar balarabe dolar amurka $1.3 Mun shirya tsaf domin kamo A.A Zaura ~Cewar hukumar EFCC.

Spread the love

Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin Nigeria zagon ƙasa ta EFCC tace ta shirya tsaf domin kama dan takarar Sanata a yankin Kano ta tsakiya cikin jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim Zaura (AA Zaura), bisa shari’ar da ake yi na zarginsa da damfara kudi kimanin dala Miliyan guda da digo uku, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kano.

Lauyan hukumar EFCC, Ahmad Rogha, ne shaidawa manema labarai a safiyar ranar Litinin, inda yace zasu kama Zaura bisa gaza halartar zaman kotun da yayi, saboda haka ya bada tabbacin cewa, lallai zasu kama shi kuma zasu gurfanar dashi a gaban kotu yayin zaman da kotun zata yi na gaba a ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2023.

EFCC na tuhumar AA Zaura ne da damfarar wani dan kasar Kuwait kudi dalar Amurka miliyan 1,320,000 (Dala miliyan daya da dari uku da ashirin) bisa zargin cewa yana sana’ar gine-gine a Dubai, Kuwait da sauran kasashen Larabawa.

A shekarar 2020 ne wata kotu ta wanke AA Zaura daga zargin, amma kuma EFCC bata gamsu da hukuncin ba, dalilin da yasa ta daukaka ƙara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button