Biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da jama’a haramun ne- Sheikh Maqari

Biyan Kudin Fansa A Haramun Ne A Musulunci, Cewar Sheik Maqari

Limamin babban masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, ya bayyana cewa biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane haramun ne a Musulunci.

Malamin, wanda ya bayyana haka lokacin Tafsirin da yake gabatarwa a watana azumin Ramadana, ya kara da cewa biyan kudin fansa zai karfafa gwiwar masu garkuwa da mutane da kuma ba su karin kudi da za su sayi makamai don ci gaba da kai hare-hare.

“Tun da Allah (SWT) ya haramta biyan kudi ga makiyi wanda yake yaki da kai, domin kada ka kara masa karfi, don haka biyan kudin fansa domin a saki wanda aka yi garkuwa da shi haramun,” in ji shi.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *