Boko Haram : ‘Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ƙungiyar 21 yayin da suka yi yunkurin sake kai hari a Geidam’

Dakarun sojin Najeriya

Rahotanni daga jihar Yobe, da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kai hari garin Geidam kwana guda bayan sun yi wa garin tsinke.

Majiyoyi sun ce ranar Asabar din nan ne mayakan suka sake shiga garin, inda suka shafe sa’o’i a suna artabu da sojojin Najeriya, har zuwa dare.

Majiyoyi sun shaida wa BBC Hausa cewa wasu mutanen da ke zaune a garin sun rika tserewa domin tsira da rayukansu yayin da lamarin ke faruwa.

Majiyoyin sun ce mayakan sun fasa shaguna da dama, kana suka yi awon gaba da kayan abinci mai yawa, kamar dai yadda suka yi lokacin da suka kai hari a ranar Juma’ar data gabata.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya Birgediya Janar Muhammed Yarima, ya bayyana wa BBC cewa ‘yan Boko Haram din sun shiga cikin jama’a, don haka suna fuskantar matsala wajen gano su don yaki da su.

”Matsalar ita ce sun shiga cikin unguwanni, sai muka yi shawarar cewa a tsaya tukunna sai an kaɗa su waje, sai a far musu” in ji kakakin rundunar sojin Najeriyar.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *