Labarai

Bola Tinubu ya bayyana zaben Obasonjo Jonathan da Buhari amatsayin zaben da ‘yan Nageriya suka yi na kuskure a baya.

Spread the love

A ranar Laraba ne aka fara yakin neman zabe a hukumance, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya roki ‘yan Najeriya da su yi koyi daga ‘kuskuren da Suka yi a baya na zaben shugabanni.

Mista Tinubu, tsohon gwamnan Legas, a wata sanarwa a ranar Laraba, ya kuma bukaci jama’a da su kasance masu “hikima da fahimi” yayin da suke shirin zaben shugaban kasar na gaba, a zaben 2023 mai zuwa.

“Dole ne mu nuna cewa mun koya daga kura-kurai a baya. Dole ne mu kasance a shirye don yanke shawara mai wuya. Dole ne mu zama masu hikima, dole ne mu zama masu hankali; dole ne mu zabi ci gaba. Dole ne mu fifita hankali fiye da ra’ayi,” in ji Mista Tinubu a wani sako na bikin fara yakin neman zaben shugaban kasa a 2023 a hukumance a fadin kasar nan.

A Jiya ne hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta dage haramcin yakin neman zaben jam’iyyun siyasa gabanin zaben shekara mai zuwa a hukumance.

INEC, a karshen makon da ya gabata, ta fitar da kuma buga sunaye da cikakkun bayanai na ‘yan takarar jam’iyyun siyasar da suka cancanci shiga zaben

Tinubu, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) ana ganin su ne kan gaba a cikin ‘yan takara 15 da ke fafutukar karbe mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari mai ci.

Tun lokacin da tsohon gwamnan Legas ya shiga takarar neman ya gaji Mista Buhari, yanayin lafiyarsa ya kasance babban abin damuwa ga ‘yan Najeriya da dama, musamman ma masu sukar lamirin da ke nuna cewa ya dace da shugabancin kasar da ke alfahari da kanta a matsayin ‘katuwar Afirka.

Obasonjo Yar adua Jonathan da Buhari ne shugabannnin da Suka mulki Nageriya tun bayan dawowar Mulkin Dimokuradiyya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button