Budurwa Ta Fasa Auren Saurayinta Bayan Ya Biya Kusan N1m Na Kudin Aurenta

Wata ‘yar Najeriya tana tsaka da shan suka a dandalin sada zumunta bayan ta fasa aurenta.

Da take bayar da labarin, wata mata da aka bayyana sunanta da Amanda Chisom a shafin Facebook, ta ce matar (wacce ba ta bayyana ainihi kowacece ba) ta aika mata sako kan yadda ta sa saurayin da bashi da karfi ya biya kudin aure kusan miliyan.

Ta rubuta: “Don haka wannan budurwar a cikin akwatin sakona a yau ta sanya wannan mutumin wanda ba mai kudi ba ne kashe kusan miliyan don ya aure ta kawai sai ga shi ta fasa auren.

“Me zai faru da kudin da ya kashe a kan dangin ta da ke kwadayayyu saboda idan dan uwana ya zo gida da wannan jerin abubuwan bukata don ya auri ‘yar kowa zan tambaye shi idan suna ba da hannayen jari ne da ita.

Shin bai kamata ya kai karar ta ba akan karya alkawari. Ta yaya mutum zai zama mugu haka?”

“Baya ga wannan jerin, darajar mace ta gari ba za a iya kayyade shi ba, kana iya siyar da duk abin da ka mallaka don ka aure ta amma lalatacciyar mace, hmmmm.

Kar ka yi ko kusa koda sun ba ka ita kyauta da asusun tallafi na dala miliyan.”

Loveth Oge yayi sharhi:

“Masu laifi … ne duka dangin. “Duk wanda sunansa ya bayyana a wannan takarda dole ne a kama shi kuma su biya kudin daya bayan daya.” Umezulike Desmond-Cruz ya yi martani: “Idan kun bani irin wannan takardar …

“Zan yaga shi a gaban dukka magabatan sannan in fadawa wacce zan aura din ta same ni a cikin gidana domin taron gaggawa.

“Sakamakon wancan taron ne zai nuna in zan aure ta ko ba zan yi ba.”

Daga Ahmad Aminu Kado

One thought on “Budurwa Ta Fasa Auren Saurayinta Bayan Ya Biya Kusan N1m Na Kudin Aurenta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *