Labarai

Buhari ba zai iya wanke ka a idon ‘yan Nageriya daga zargin safarar miyagun kwayoyi ba ~Atiku Ga bola Tinubu

Spread the love

Kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa, ta caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kan jawo shugaban kasa Mohammadu Buhari cikin yakin neman zabensa.

Jam’iyyar PDP ta ce yunkurin da Tinubu ya yi na amfani da Buhari wajen yi wa hotonsa fenti ba zaiyi Nasara ba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin yakin neman zaben Atiku-Okowa, Kola Ologbondiyan a Abuja, ranar Asabar.

Ya ce, “Hakika abin dariya ne ace Asiwaju Tinubu wanda aka yiwa lakabi da safarar miyagun kwayoyi da tabo na rashawa da yawa a yanzu yana neman shugaba Buhari a yakin neman zabensa bayan ya yi takama da cewa shi (Shugaba Buhari) ba shi da wata alaka da siyasa kuma ba zai iya zama shugaban kasa ba. har sai da shi (Tinubu) ya kawo masa dauki.

’Yan Najeriya sun kalli yadda Tinubu ya tozarta Shugaba Buhari har ma ya nuna yadda a cewarsa, Shugaba Buhari ya yi kuka bayan ya sha kaye a zabe har sau uku har sai da (Tinubu) ya dauke shi, ya share hawayensa ya nada shi Shugaban kasa.

“Saboda haka ‘yan Najeriya suna mamakin ko wace rawa Tinubu, wanda ya raina Buhari da cewa ba shi da kima a siyasance, a yanzu yake son Shugaba Buhari ya taka rawar gani a yakin neman zaben da ya ke jan shi a fage, idan ba don ya shafa wa Mista Shugaban kasa kazanta ba.

“’Yan Najeriya na mamakin ko me shugaba Buhari, tare da nuna kyama ga al’amuran da suka shafi almundahana da shaye-shayen miyagun kwayoyi, zai ce yayin da yake gabatar da Asiwaju Tinubu ga masu zabe a wajen taro

“Shin ko shugaba Buhari zai bayyana wa ‘yan Najeriya alakar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi da miyagun kwayoyi wanda wata kotun da ke da hurumin shari’a a Amurka ta bayar da umarnin a kwace wasu makudan kudade da suka kai dala 460,000 da aka samu a asusun Tinubu a matsayin wata haramtacciyar mu’amala?

“Shin Buhari zai nemi afuwar ‘yan Najeriya kan amincewa, a matsayinsa na shugaban kasa na soja, a aiwatar da hukuncin kisa kan wasu ‘yan Najeriya da suka aikata laifukan da suka shafi muggan kwayoyi sai dai a yanzu an gabatar da wanda ya batar da kudi a cikin al’amarin da ya shafi muggan kwayoyi a matsayin shugaban gwamnatin tarayyar Najeriya?”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button