Labarai

Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don bayar da Naira Biliyan 402

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wasu wasikun bukatu daban-daban, a jiya Talata ya nemi amincewar majalisar dattijai domin fitar da kudaden alawus-alawus da ya haura Naira biliyan 402.

Farkon irin wannan bukatu da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar, shi ne Naira biliyan 375 da aka ware domin warware matsalolin masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Sauran irin wannan bukatu na biyan basussukan da za a bi ta ofishin kula da basussuka (DMO), sun hada da Naira biliyan 6.706 na gwamnatin jihar Kebbi kan aikin gina titin tarayya a jihar da kuma Naira biliyan 2.706 na gwamnatin jihar Taraba domin gina hanyoyin tarayya.

Shugaba Buhari a wata bukata kamar yadda Lawan ya karanta a zauren majalisar, ya kuma nemi amincewar majalisar dattawa kan bayar da Naira biliyan 18.623 ga gwamnatin jihar Kebbi.

Shugaban a cikin wasikar ya ce biyan Naira biliyan 18.623 ga gwamnatin jihar Yobe ta hannun ofishin kula da basussuka (DMO), zai taimaka wa jihar wajen biyan duk wasu kudade da aka kashe wajen aiwatar da ayyuka biyar na gwamnatin tarayya a jihar.

Shugaban a cikin wasiƙun daban-daban, ya nemi yin la’akari da buƙatun cikin hanzari.

A wata wasikar bukatar shugaba Buhari ya nemi a tabbatar da nadin Mohamed Sabo Lamido a matsayin kwamishinan zartarwa, kudi da kuma asusu na hukumar kula da harkokin sama da kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button