Labarai

Buhari ya nemi amincewar majalissa akan karin Naira biliyan 442.72 na tallafin man fetur da yayi.

Spread the love

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga Afrilu, Buhari ya ce karin kudin da aka samu da Naira biliyan 442.72 daga Naira Tiriliyan 3.557 zuwa Naira Tiriliyan 4 ya zama dole yayin da ake fama da ci gaban tabarbarewar tattalin arziki, ciki har da karin farashin danyen mai a kasuwa da yakin Rasha da Ukraine ya yi.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya suke shan wahala wajen samun man fetur din.

A halin yanzu dai yawancin jidajen mai a biranen Najeriya a rufe suke, wanda hakan ya tilastawa talakawa siyan man mai tsada a wajen ‘yan bunburutu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button