Buhari ya sauke sufeton ‘yan Sanda ya Kuma Nada DIG Usman Alkali.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin DIG Usman Alkali Baba a matsayin mukaddashin sufeto janar na ‘yan sanda.

Ministan Harkokin ‘yan sanda, Mohammed Maigari Dangyadi, ya sanar da wannan a ranar Talata, yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Kasa.

Ya ce nadin Baba ya fara aiki nan take.

Shugaba Buhari ya kara a ranar 4 ga Fabrairu, 2021, ya kara wa’adin Mohammed Adamu a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP) na tsawon watanni uku.

Adamu ya kasance, duk da haka, ya kwashe watanni biyu da kwana uku daga cikin karin watannin uku kafin nadin Baba.

Nadin IGP mai rikon kwarya ya dogara ne da amincewar taron Majalisa da a ake sa ran gabatarwa nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *