Labarai

Buhari Ya Tashi Zuwa Kasar Mauritaniya Domin Karbar Kyautar Zaman Lafiya

Spread the love

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya ce kungiyar zaman lafiya ta Abu Dhabi za ta ba shugaba Buhari lambar yabon.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Nouakchott ranar Litinin don karbar lambar yabo ta “African Award for Strengtheing Peace” a babban birnin kasar Mauritania ranar Talata.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, an ba da kyautar ne saboda rawar da shugaban ya taka wajen samar da zaman lafiya a nahiyar.

Adesina ya ce taron zaman lafiya na Abu Dhabi ne zai ba wa Shugaba Buhari lambar yabon, taron shugabannin da aka kafa a shekarar 2014 domin bibiyar sabbin hanyoyin rungumar ‘yan kasa baki daya, da samar da dawwamammen zaman lafiya, da kuma kokarin samar da duniya mai aminci da dorewa ga kowa da kowa. .

Kafin karbar lambar yabon, mai taimaka wa shugaban kasar ya ce Buhari zai shiga cikin shirin dandalin zaman lafiya na Afrika karo na uku, inda zai gabatar da jawabi kan muhimman abubuwa da nasarorin da aka samu a shirin samar da zaman lafiya a Afirka.

Shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya); Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Mohammed Monguno (mai ritaya); da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Amb. Ahmed Abubakar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button