Buhari zai gana da likitansa a Faris ranar Asabar

Shugaba Buhari Zai Gana Da Likitansa A Faris Ranar Asabar

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a ranar Asabar don ziyarar aiki zuwa Paris, babban birnin Faransa.

Manyan majiyoyi sun ce Shugaban zai kasance a Paris na akalla kwanaki hudu, inda kuma aka shirya zai gana da likitansa a can.

“Buhari zai yi tafiya zuwa Paris na tsawon kwanaki hudu. Kuma zai je Kampala babban birnin Uganda, sannan zai lula ƙasar Burtaniya don ganin likitocinsa amma daga bisani su likitocin sun zabi haduwa da shi a Paris ranar Asabar.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *