Buhari Zai Kashe biliyan 6.45 domin gina cibiyoyin samar da iskar shaƙa ga marasa lafiya a wurare 38 na Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da naira biliyan 6.45 domin gina cibiyoyin samar da iskar shaƙa wa marasa lafiya a wurare 38 na Najeriya.

An amince da waɗannan kuɗin ne a yunƙurin gwamnatin ƙasar na yaƙi da annobar korona.

Batun amincewar ya fito ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziƙi Ta Najeriya wadda Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta tare da gwamnoni da Ministan Abuja da Gwaman Babban Bankin Najeriya da sauran manyan jami’an gwamnati, kamar yadda kafar sadarwa ta BBC ta ruwaito.

Haka kuma Shugaba Buharin ya bayar da umarnin sakin miliyan 255 domin gyara cibiyoyin samar da iskar a asibitoci biyar da ke ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *