Cikin Bakin Ciki da 6acin Rai Ganduje ya nemi Jami’ar Amurka data nemi gafarar sa.

Gwamnatin jihar Kano ta nemi Jami’ar Amurka da shuwagabannin jami’ar ta East Carolina su nemi gafarar sa kan wani mukami da ya jawo ce-ce-ku-ce da aka baiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Babban Malami mai ba da shawara da kuma zuwa amatsayin cikakken farfesa kan harkokin mulki da al’amuran duniya a jami’ar a ranar 30 ga Nuwamba 2020.

Wata sanarwa daga Sakataren Gwamnatin Kano (SSG), Alhaji Usman Alhaji ya kuma nemi a dauki matakin ladabtarwa a kan malamin da ya tayar da rikicin wanda ya yi yunkurin kunyata gwamnan da mutanen kirki na jihar ta Kano.

Ya ce duk da cewa gwamna ko wani jami’in gwamnatinsa ba su da wata hujja ta shakkar gaskiyar wasikar da daya daga cikin malaman jami’ar ta aiko, wacce aka sanar da ita ta hanyar amfani da kayan aikin jami’ar,

‘’ Mun yi matukar bakin ciki game da hayaniyar da ta biyo bayan wannan nadin mukamin da ya yi kokarin kunyata gwamnan da mutanen kirki na jihar Kano, ”sanarwar ta kara da cewa.
Alhaji Usman ya yi nuni da cewa, Gwamna Ganduje ya samu takardar shedar kammala karatun ilmi a kasa (NCE) 1972, kuma ya yi karatun Digiri na farko a kan ilimin Kimiyya daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, 1975; Digiri na biyu a Fannin Ilimi a Jami’ar Bayero, Kano (BUK) 1979; da kuma Gudanar da Jama’a kuma daga ABU 1985, da kuma Ph.D. wanda ya samu kusan shekaru talatin da suka gabata daga Jami’ar Ibadan da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Hukumar ta SSG ta ce idan aka yi la’akari da wannan matsayin na masanin Gaskiya Gwamna zai kasance mutum na karshe a duniya da ba ya rokon ko yarda da almundahanar mukami a cikin wata jami’a ko kuma babbar jami’ar ilimi a ciki da wajen Najeriya.

Yayin da ake yi wa jami’ar fatan alheri, sanarwar ta nuna matukar kaduwa kan abin da wasikar ta fito daga Ofishin Shugaban da kuma Babban Mataimakin Shugaban Kwalejin na Jami’ar, inda suka amince da kuskure wajen isar da sakon da ke sanar da nadin.

ALHAJI USMAN ALHAJI
Sakataren Gwamnatin Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *