Cin hanci da rashawa bazai bar Nigeria taci gaba ba ~ Ganduje

Gwamman Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Nigeria baza ta cigaba a irin wannan yanayi da cin-hanci da rashawa ya mamaye ko Ina ba.

Gwamman ya bayyana hakan ne ayau Alhamis yayin rantsar da sabon kwamiti wanda ya ƙunshi mutane takwas domin ƙarkafa yaƙar cin hanci da rashawa a faɗin Jihar ta Kano.

Ganduje wanda ya samu wakilcin Alhaji Usman Alhaji, babban sakataren gwamnatin Jihar, ya ƙara da cewa babu wani babban yunƙurin da gwamnatin Jihar take face na tabbatar an magance matsalar cin-hanci da rashawa tsakanin al’umma.

Babu buƙatar ayi ƙarin biyani dangane da yadda cin-hanci da rashawa ya mamaye Nigeria, kuma a haƙiƙanin gaskiya ba zamu taɓa cigaba a irin wannan yanayi na yawaitar almundahana ba “Ganduje ya bayyana”.

Ya kuma ƙara da cewa babban burin su a Jihar Kano shine na rage kaifin cin-hanci ta hanyar nuni/koyarda gaskiya da riƙon amana a tsakanin alummar Jihar.

A gefe guda kuma kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, Gwamnan ya yabawa hukumar karɓar koke-koke da magance cin-hanci da rashawa wato (Public Complaints and Anti-Corruption Commission) wadda Muhyi Magaji Rimin-Gado yake jagoranta bisa ga irin namijin kokarin da suke wajen yaki da cin hanci a Jihar Kano.

A ƙarshe yayi kira ga sabbin ma’aikatan da gwamnatin ta rantsar da su zage damtse wajen gudanar da aikin su cikin gaskiya, jajircewa da riƙon amana domin amfanuwar Kano da jama’ar jihar baki ɗaya.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *