Cin Hancin Milyan Ashirin N20m masarautar Kano ta bani domin na daina binciken badakalar filayen ~Inji Muhuyi Magaji.

Shugaban Kwamitin Koke-koke da Yaki da Cin Hanci da Rashawa na Jihar Kano, Barista Muhuyi Maagji Rimin Gado, ya nuna cin hancin Naira miliyan 20 da ake zargin an ba shi don ya daina binciken badakalar filaye da ya shafi Majalisar Masarautar Kano.

Hukumar na binciken masarautar kan zargin sayar da fili mai girman hekta 22 a Gandun Sarki, Dorayi Karama, da ke karamar hukumar Gwale ta jihar.

Muhuyi ya yi zargin cewa kudaden sun biya filaye inda aka karkatar da su zuwa wasu aljihunan masarautar, wanda hakan ya sanya wasu mambobin majalisar cikin matsala.

0 thoughts on “Cin Hancin Milyan Ashirin N20m masarautar Kano ta bani domin na daina binciken badakalar filayen ~Inji Muhuyi Magaji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *